Labarai Da Dumi Dumi

FARANSA DA JAMUS ZASU TATTAUNA AKAN BITCOIN








bitcoin



Kasar Faransa da kasar Jamus zasu zauna don yin shawarwari kan ka'idojin bitcoin a taron G20
da za'a gabatar a kasa Ajentina.


Ministan kudi na kasar Faransa Bruno Le Maire ne ya bayyana haka a ranar Alhamis da ta gabata, yace shi da takwaransa na kasar Jamus zasu tattauna domin daidaita tsarin bitcoin,a taron koli na manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 wanda za'a gudanar a watan Maris a kasar Ajentina.


Ya ci gaba da cewa "Za mu sami haÉ—in gwiwa tsakanin Fransa da Jamus game da hadarin da ake danganta shi da bitcoin, ka'idojin shawarwarin kuma za a gabatar da su a matsayin takardar hadin gwiwa ga takwarorinmu na G20 a wajen taron"

Mafi girma da kuma shahara a kudaden zamani na cryptocurrency a duniya wato bitcoin ya fadi zuwa rabin farashin sa a 'yan kwanakin nan.


"Muna da alhakin yin bayani ga jama'armu don rage hadarin da za'a iya samu a cinikayyar bitcoin," in ji mai magana da yawun Jamus mai suna Peter Altmaier a taron manema labarai a birnin Paris.

No comments