Labarai Da Dumi Dumi

Masu Zuba Jari A Hadadar Kudaden Yanar Gizo Zasu Fara Biyan Haraji A Indiya.

kudaden cryptocurrency


Gwamnatin kasar Indiya ta aika takardun haraji zuwa ga masu zuba jari a asusun ajiyar kuÉ—aden yanar gizo wanda aka fi sani da cryptocurrency a turance, yayin da hadahadar kudaden ta kai kimanin dalar Amurka biliyan 3 da miliyan 500.

Gwamnatin kasar ta aike da takardun ne ga dubun dubatar 'yan kasar da ke da alaka da hadahadar.

Hakan ya biyo bayan binciken da babban ofishin binciken asusun ajiyar kudaden shiga na kasar ya gudanar, inda ya gano anyi hadahadar biliyoyin kudaden a cikin watanni 17 kacal.

No comments