Labarai Da Dumi Dumi

Hukumar JAMB Ta Sanar Sababbin Ranakun Jarabawar UTME Na 2018




Farfesa  Ishaq Oloyede, rajistara na hukumar hadin gwiwa da shirya jarabawa don masu neman gurbin karatu a jami'i'o da makarantu na gaba da sakandire, wato JAMB, ya bayyana cewa za'a gudanar da jarrabawar tantancewa UTME ta 2018 a tsakanin 9 ga watan Maris zuwa 17 ga watan.

Oloyede ya ce za a gabatar da jarrabawar ta UTME din ne bayan jarabawar gwaji wato mock da aka shirya,a farkon makon Fabrairu.

Ya yi jawabin ne a yayin ganawar sa da masu ruwa da tsaki akan batun: "Shirye-shiryen da aka tsara a kan yadda za a gudanar da jarabawar tantacewa ta shekarar 2018," a ranar Talata da ta gabata.

Shugaban Hukumar ta JAMB ya bayyana cewa an shirya gudanar da jarabawar a tsakanin 22 ga watan Janairu zuwa 24 ga watan. Mun sauya rakanakun jarabawar ne sakamakon ci gaba da yajin aiki da ma'aikatan jami'o'i ba masu koyarwa suka yi.

Ya kara da cewa; , "Ba za mu iya samun dama ga cibiyoyin CBT ba domin mafi yawansu suna cikin jami'o'i wadanda yawancinsu ke qarqashin kulawar ma'aikatan jami'o'in ba masu koyarwa.

Oloyede ya kiyasta cewa kimanin kashi 10 cikin dari na masu neman gurbin karatu a jami'o'i na wannan shekara, sunyi rajista domin jarabawar ta UTME, ya kara da cewa; kimanin mutum 283,319 sukayi rajistar a wannan karon.

Yayi  gargadi  game da amfani da abubuwan da aka haramta a lokacin gudanar da jarabawar. A cewar shugaban na hukumar JAMB, an  haramta shiga da kayan da bai dace ba, ga masu rubuta jarabawar da kuma masu kulawa da su. Ya kara da cewa, 'an yarda kawai a shiga da agogon hannu da kuma kayan rubutu kamar fensuri na HB.

No comments