Labarai Da Dumi Dumi

Shugaban Kasa Buhari ya roki Al'ummar Benue da su dauki makiyaya a matsayin yan uwansu, saboda Allah

Shugaban Kasa Buhari ya roki Al'ummar Benue da su dauki makiyaya a matsayin yan uwansu, saboda Allah

Buhari ya roki gwamnatin Benue da mutanen gari da su dauki wannan kashe kashe ya zama kaddara a gare su.

Shugaban kasan ya kara da cewa, mutanen Benue su dauki makiyaya a matsayin yan uwansu,  ya Kuma daukan musu alkawarin cewa Gwamnati Za tayi kokarin ta wajen ganin an kamo wadanda suka yi wannan ta'addancin.

Yayi wannan Alkawarin bayan ziyarar da  shugabannin siyasa, sarakunan Benue suka kai masa a yau litinin karkashin jagorancin Gwamna Ortom a fadar shugaban kasa a Abuja

Shugaban kasa ya basu tabbacin cewa shugaban rundunar yan sanda da jami'an sirri (DSS)  zasuyi iya kokarin su wajen ganin an kamo yan ta'adda.

Ina kara rokon ku, da ku karbi makiyaya a matsayin yan Kasa masu yanci, shugaban kasa ya kara cewa.

No comments