Kungiyar Kwallon Kafa Ta Man City Tana Sa Ran Sayan Alexis Sanchez Duk Da Kutsen Da Man UTD Tayi A Cinikayyar
Babbar kungiyar kwallon kafar ta premier league din zata cigaba da sasantawa da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, duk da cewa sun matsa akan cewa bazasu biya Arsenal din £35 miliyan din da suke so su saida dan wasan ba.
Har ila yau shirin Man City akan sayan dan wasan be chanja ba, duk da kutsen da 'yan adawarsu da suke gari daya sukayi ranar alhamis dinnan da ta gabata, dadin dadawa kuma Man City din suna kokarin sayan wani dan wasan banda Alexis.
An samu rahoto a ranar alhamis cewa Man United sunje da kudirin sayan Alexis ga Arsenal, duk da cewa majiyoyi masu karfi daga manyansu wato kungiyar kwallon kafa ta city basu sani ba ko wasa da sana'a ake nema ayi musu - daga bangaren ejojin ko abokan adawarsu.
No comments