Labarai Da Dumi Dumi

WANI KWAMISHINA YA BUKACI MAGOYA BAYANSA DA JEFI TSOHON GWAMNAN KANO


Wani faifan bidiyo da ake tunanin ya fita daga hannun kwamishinan ayyuka wato Abdullahi Abbas ya bayyana, inda yake umartar magoya bayansa da su jefi tsohon gwamnan jihar kano kuma sananta a yanzu wato Rabi'u Musa Kwankwaso a yayin wata ziyara da zai kawo a karshen watan nan da muke ciki.

Duk da dai har yanzu kwamishinan bai fito karara ya bayyana alaka ko rashinta da wannan bidiyo ba, sai  dai bayyanar sa na cigaba da yamutsa hazo tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan da kuma gwamna na yanzu, Abdulllahi Umar Ganduje. Wannan kuwa, na da alaka ne da rashin jituwar da ke tsakanin Sanata Kwankwason da kuma gwamna Ganduje wadda ta shafe 'yan lokuta. Hakan kuma ya Kara bunkasa sukar ra'ayi da kace nace tsakanin magoya bayan tsagin guda biyu.
Faifan bidiyon na kunshe ne a harshen hausa, inda aka ambaci tsohon gwamna a mastayin 'shedanin siyasar kano' tare da bada umurni ga magoyan Abdullahi Abbas din, da su tanadi duwarwastun jefe tsohon gwamnan yayin isowar sa jihar Kanon yain da a waje guda kuma, yake Kara tabbatar da hannunsa dumu-dumu wajen shirya wa tsohon gwamnan hare-hare a kwanakin baya.
Wasu daga cikin kalaman da suka fita a faifan bidiyon sun hada da yake cewa"A yanzu, shugbansu wato kwankwaso zai zo kuma za mu tarbe shi a Kwanar Dangora ko kuma a Dakatsalle, za ku iya sanin bayan aikin hajjin da musulmi da gudanar wa akwai jifan shedan, to don haka sai ku jira sanarwar ranar da za ku jefi shedanin siyasar jihar Kano. Ba ma jin tsoron kowa, za kuma mu iya kai wannan dambarwa har dakin sa. A karshe, 'yan uwana muyi aiki tare, domin mu tarwatsa Kwankwaso, kun riga kun sani tsoron mu yake ji".

No comments