Fulani sun maka Laifi, sannan muna baka hakuri - Gwamna Shettima
MUNA HADAKA DA GIRMAN ABUN BAUTARKA, KADA KA FITA DAGA CIKIN KUNGIYAR GWAMNONIN AREWA, SAKAMAKON KISAN KIYASHIN DA FULANI SUKAYIWA AL,UMMARKA.
Inji Gwamnan Borno Kashim Shettima
Gwamnan Borno Shettima ya roki gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, akan yayi hakuri ya jure, kuma ya yafewa mutanen Arewa, akan mummunan aikin da fulani suka aikata a jiharsa, sannan kada hakan yasa shi Gwamna ortom yayi fushi har ya fice daga Kungiyar tasu ta gwamnoni.
Munsan cewa babban laifi fulani suka aikata a jihar ka, hakan ne ma yasa muka taso kafa da kafa don mu baka hakuri tare da lallashin ka, mu kuma nuna maka cewa muna tare da kai da kuma al,ummar jihar ka Tivawa, Inji Gwamna Kashim Shettima
No comments