Majalisar Ministoci Ta Amince Da Gina Tashar Wutar Lantarki A Filin Saukar Jirage Na Abuja
Majalisar Ministoci Ta Amince Da Gina Tashar Wutar Lantarki A Filin Saukar Jirage Na Abuja
A zaman majalisar ministoci na farko a sabuwar shekara a karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari, majalisar ta amince da gina tashar wutar lantarki mai zaman kansa a filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Da yake karin haske kan zaman majalisar, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya ce an dauki matakin ne don kawo karshen matsalar hasken wutar lantarki da ake fuskanta a filin saukar jiragen saman.
No comments