Labarai Da Dumi Dumi

KWALLIYAR YAN AREWA TARE DA AL'ADUNSU


Ala'dun arewa yasha banban dana sauran kasashe, inda yanayi yake zuwa ya tafi, yanayin kwalliya a najeriya yanada alaka da asalin kasar, duk yayinda akayi sabo zaku gane shi da al'adun gargajiya.

Hanyoyin al'adun arewa sune misalai masu kyau na yadda yan najeriya ke girmama al'adunsu. Idan ka duba yanayin kayan yan matan arewa yanzu zaka gane cewa kusan duka yanayin dinkunan su dogaye riguna ne.

 Atamfar Arewa

Atamfa tana da wani nau'i na musamman wanda yawancin kayan ado na arewa da ita ake amfani, idan kanada telan da ya kware a dinki kuma kasan irin tsarin dinkin da kakeso, dinkin atamfar ka zata zoma cikin sauki, sannan kuma atamfa tana da saukin hadawa dan haka zaka iya kirkirar ko wani tsari ba tare da wani wahala ba.

Kwalliyar Arewa

Ba atamfa kadai aka san arewa dashi ba, akwai wasu al'adun  masu kyau, daya daga ciki shine zane-zane da akeyi a jiki. yawancin wadannan zanen anayinsu ne saboda bukukuwa da sauran abubuwa da suka faru na musamman. Tare da taimakon wasu nau'o'in Arewa, zaka iya Æ™irÆ™irar É—akin tufafi da aka saba da al'adun Arewa.

2 comments: