Labarai Da Dumi Dumi

'Yan makaranta 22 da ke kan Hanyar tafiya Ziyarar Bude Ido sun rasa Rayukansu a Kano.

'Yan makaranta 22 da ke kan Hanyar tafiya Ziyarar Bude Ido sun rasa rayukansu a kano.

A kalla dalibai 22 na makarantar sakandare Misau a jihar Bauchi sun mutu sakamakon faruwar hadari a ranar Talata a hanyar Bauchi-Kano.

Jami'in Kwamishinan Hukumar Kare Haddura ta Kasa wato Federal Road Safety commission (FRSC) na Jihar Kano, Kabir Daura, ya ce an samu hadarin ya faru a kauyen Tsaida dake garin Gaya na jihar Kano a ranar 13 ga watan Fabrairu a misalin karfe 11:30 na safe. 'Yan makarantan suna kan hanyar Kano a dalilin kawo ziyarar bude ido daga makaranta zuwa gidan rediyo a lokacin da motar tasu tayi karo da babbar motar DAF mai zuwa daga hannun tahowa. 

Daga cikin dalibai 22 da suka mutu, 'ya'ya maza ne 12 da 'yan mata 10, an ajiye gawawwakin su a General Hospital Gaya. Sauran ukun sun ji rauni. "An kai biyu daga cikin masu raunin asibitin Gaya. Yayin da daya daga cikin su ya jigata sosai an tura shi babban asibiti a cikin garin kano," in ji Daura.

Daga Bangaren hukumar 'yan sanda na jihar kano sun shaidawa manema labarai cewa; 'yan sanda dake wajen sun tabbatar da hadarin, inda suka ce' sun kasance a wurin suna kokarin "kwantar da hankulan mutane".

Wani wanda al'amarin ya faru akan idon shi;  Tella Maiunguwa, ya shaidawa manema labarai cewa motar daliban tayi karo ne da babbar motar DAF yayin da suke Æ™oÆ™arin kauce wa wani rami. Maiunguwa ya ce hadarin ya faru ne kusa da Maitama Sule College ta Dudduru.

No comments