Bikin Auren 'yar Ganduje; Sanata Kwankwaso ya kira Ma'auratan da "zawarawa"

Jama'a suna bayyana ra'ayinsu dangane da bikin auren 'yar gwamnan jihar Kano, Fatima (Baby) Ganduje da dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi da aka kulla a ranar Asabar din da ta gabata a Kano.
Daurin aure ne da ya tara wane da
wanen Nijeriya a jihar Kano.
Jihar ta kano ta cika kwarai da manyan mutane masu rike da kujerun mulki a Nijeriya tun daga kan shugaban kasa, zuwa shugaban majalisar dattijai, zuwa gwamnoni da adadinsu ya kai 22, zuwa ministoci, zuwa jakadun kasashen duniya, mataimaka da mashawarta ga gwamnoni da shuwagabanin kasa da dai sauran masu rike da mukamai daban-daban.
Shugaba Buhari ne wakilin Fatama shi kuma jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya wakilci idrisu. Tinubu ya karbu Fatima daga Buhari a matsayin mata ga Idris kuma nan take Buhari ya biya sadakin Naira dubu 50, aka kuma daura auren.
Amma wannan daurin auren ya jawo cece kuce sosai, ta ganin yadda aka gudanar da bikin cikin wadata da kuma yadda hotuna suke ta zagayawa game suna nuni da yadda amarya da ango suke sheke ayarsu ta hanyar sumbata da runguma, duba da dai shi idrisu Ajimobi ba bahaushe ba, amma fatima bahaushiya ce kuma diyar fulani. Kowa dai yana ta tofa albarkacin bakin sa.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a ranar Asabar a yayin da ya ke ganawa da wasu ‘yan akidar Kwankwasiyya a gidansa da ke Kaduna, ya bayyana ra’ayinsa dangane da auren, inda ya kira amarya Fatima Baby da angonta Idris da ZAWARAWA.
“Mutane kadan ne ke murna da auren da auren ZAWARAWAN da aka kulla a jihar Kano, domin dai bazauri da bazaura daya ne aka yi wa aure ba da yawa aka tara aka aurar ba.”
Kwankwaso ya tuhumi masu rike kujerun mulki da suka bar ofisoshinsu don halartar auren; "a matsayin wadanda basu da abun yi".
“Na kuma ji labari cewa wannan sha’ani na auren mutum biyu kacal ya sa an hana mutanen jihar Kano fita wuraren sana’o’insu.”
“Wannan ko shakka babu ya fito da wasu abubuwa fili, wadannan abubuwa sun hada da: gaskiya da rashin gaskiya, haske da duhu da kuma wadanda suka damu da auren dubunnan zawarawa da kuma wadanda suka damu da auren iyali daya tal,” inji Sanata Kwankwaso.
No comments