Labarai Da Dumi Dumi

AN BUGE KAMFANIN WAYAR HANNU NA SAMSUNG AKAN SABUWAR WAYAR SU TA SAMSUNG GALAXY NOTE 9.

Wayar hannu ta samsung 


Kamfanin wayar hannu na Vivo dake kasar sin ya yayi makamanciyar sabuwar alama mafi kyau ta sabuwar wayar hannu ta kamfanin Samsung wato Samsung Galaxy Note 9.


Kamfanin na samsung ya bayyanar da sabuwar alamar mafi kyau ta Samsung Galaxy Note 9 ne a wajen bajakolin fasaha da aka gabatar a garin Las Vegas dake kasar Amurka.


An sa ran wayar ta Galaxy Note 9 zata zama wayar farko dake dauke da na'urar firikwensin yatsa, amma hakan bai kasance ba dalilin bayyanar sabuwar wayar Vivo a bajakolin fasaha na garin Las Vegas, wadda take dauke da makamancinyar na'uarar samsung Note 9.


Kamfanin ya yi iʙirarin cewa fasaha ta nazarin yatsa na nuni ya fitar da wasu ingantattun maganganun da aka samo don wayoyin salula a hanyoyi da dama.


Babban mataimakin shugaban kamfanin Vivo, Alex Feng ya ce: "Tare da kokarinmu na bincike mai yawa da kuma zuba jarurruka na R & D na tsawon lokaci, Vivo yana da matukar matsayi don yin hidima a kan ci gaba da fasahar sikelin zane-zane. Muna matukar farin cikin samar da sabuwar wayar a kankanin lokaci.

No comments