An kashe Makiyayi a garin Ekiti, Gwamna Fayose ya kira zaman lumanan gaggawa
Gwamnatin Jihar Ekiti, tana cikin rudani a kisan wani makiyaye da akayi mai suna Babuga Dengi, a ranar litinin da ta gabata a cikin garin Oke Ako dake Ikole dake karamar hukumar Ikole a Jihar Ekiti. Bayan wannan kisan day a gabata a garin, Gwamna Fayose ya kira zaman lumana na gaggawa ranar talata domin ganin wannan kisa bai haifar da kasha kasha a jihar sa ba.
A fadar Gwamna Fayose yace, wanda suka kasha wannan makiyayi ba wasu bane illa kabilar TIV dake Jihar Benue amma mazauna Ekiti, wadan da suke noma a bangaren Ekiti.
Fayose ya kira zaman lumana na gaggawa tsakanin Fulani da kabilar TIV mazauna Ekiti, a garin Ado Ekiti, ya kara da fada musu cewa ba zai yarda da kashe kashe a Jihar sa ba, sannan kuma yayi alkawarin wanda yayi wannan kisan za’a kamo shi a gurfanar das hi a gaban kuliya.
A da dai Fayose yayi kira ga al’ummar da suke garin Ekiti na cewa duk wanda yaga wani makiyayi ya kashe shi, amma a yanzu ya janye da wannan kalamin na sa. Fayose yayi Alla wadai da kisan day a auku a garin Benue a kwanakin Baya.
Sannan yace bazai yarda da wani ya kawo masa damuwa a cikin jihar sa ba, saboda ko kai Bafulatani ne, ko TIV , ko kuma wani yare daban mazauni a Ekiti, suna maka maraba.
Yayi wannan Magana a gaban Shugabannin Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, Manoma, yan farauta, jami;an tsaro, da kuma wakilai daga kabilar TIV. Fayose yace an zabe shi ne domin ganin an sami zaman lafiya a jihar shi ba rigima ba. Ya ja kunnen Fulani da TIV akan kar su yarda su mayar masa da Jihar dandalin filin Yaki, domin bazai yarda da wannan abun ba.
“In har ka kasha to tilas sai mun kamo ka an kasha ka” inji Fayose
No comments