Labarai Da Dumi Dumi

DUK WANI SHARRI DA KAGE DA MUNAFINCI KUYI KU GAMA,KWANKWASO SAI YASHIGO JAHAR KANO A 30/1/2018



DUK WANI SHARRI DA KAGE DA MUNAFINCI KUYI KU GAMA,KWANKWASO SAI YASHIGO JAHAR KANO A 30/1/2018

Muna kara sanar da gwamnatin jahar Kano cewa munkwana da sanin yadda suke takai kawo domin ganin sun hana Shugaba Adali zuwa mahaifarsa Kano. 

Kamar yadda mukaji kwamishina a wannan gwamnatin Yana Umartar mutanensu dasu farmaki jagororin kwankwasiyya na jahar Kano a yan Kwanakin nan,wadda shi wannan kwamishina yafara kaddamar da wannan hari a Jiya Ga Kanin sa wadda suke Ubadaya,wanda wannan hari yakasance mai muni domin shi wannan kwamishina yasa 'ya'yansa na cikinsa sun farmaki Kanin mahaifinsu domin yana bin maigirma Jagora Dr. Rabiu Musa Kwankwaso. 

Hakika wannan lamari yaban mamaki domin tundaga Ranar da shi wannan kwamishina yabada wannan Umarnin ga tsirarun mabiyansu banji Kwamishinan yan Sandan jahar Kano yayi wata magana akai ba,domin wannan furici nasa Hakika barazana ne ga tsaron jahar Kano Bakidaya. 

Sannan kuma munsan anaso ayi anfani da wannan kwamishina ne domin kafa hujja akan taron da yan kwankwasiyya zasu gudanar a Ranar 30/1/2018 domin a dagatar da wannan taro.

Muna kira ga Jami'an tsaro dasu gayyaci wannan kwamishina domin jamasa kunne akan irin wannan Kalamai dayake a wannan Jaha domin samun tabbatuwar zaman lafiya a jahar Kano, Sannan kuma muma zamu zuba ido muga wane mataki za'adauka akan wannan kwamishina. 

Yan Kwankwasiyya ma'abota zaman lafiya ne kuma masu san ganin Kano da Nigeria tasamu cigaba mai dorewa. 

Domin mu yan kwankwasiyya a tsarin tafiyarmu babu inda jagoranmu yace mudau doka a hannun mu koda an cucemu shiyasa muke girmama doka da oda,kuma ba gudu baja dabaya jagoran mu Jagoran talakawan Nigeria Dr. Rabiu Musa Kwankwaso zai shigo jahar Kano a 30/1/2018.

Daga. 
Usman Kwankwason Rijiyar lemo. 

P.R.O KR/KN/0007
*@KWANKWASIYYA REPORTERS NIGERIA*

No comments