BAHARI BAZAI KAI LABARI BA A 2019
Jam’iyar adawa ta,PDP sunce gwamnonin suna garzayawa Abuja dan su sami Buhari saboda irin Abubuwan dake faruwa dan gane da rashin daukan mulkin da mahimmaci,hakan zaisa Buhari fadi a 2019.
Jam’yar tayi wannan hasashen ne Aranar Lahadi a Abuja,daga bakin sakataren kula da manufofin jama’a ta PDP,a cewar Kola Ologbondiyan.
Jam’iyar ta kara da cewa APC yakamata tahi sauri bayyana kanta awajen yan najeriya,ta hanyar gudanarda,zabe ingantacce,akana nan hukumomin jahoyin,akarkashin jahohin.
Har ila yau jam’iyar tace najeriya ta kara haduwa rashin kula a gwamnatin apc,ta gudanar da ingattacen multki.
Amaimakon fuskantan jam’a,gwamnonin apc suna tsoron yin hakan saboda abun kunyan da yake gabansu,suna garzayawa abuja domin neman taimako,sun manta da cewa shima Shugaba Muhammadu Buhari yana takansa saboda abin yake gabanshi na faduwa azabenn shekara ta 2019.
Apc ta san cewa bazata iya fuskan tan mutane milliyan takwas 8 ba, wa yanda suke fama da rashin aikin yiba ta siyasar su,kuma sunsan cewa tambayoyi na gabansu na dubban ma’aikata,aka musu kora na babu sani ba tsammani,awasu garuruwan da apc take mulki kamar,Kogi da Kaduna.
APC bazata iya dawowa mulki ba wadannan jahohin da sukasa yin komai wajen yima mutane aiki,da kuma tsadar rayuwa da jama’a suke ciki.
Hakazalika sunkasa iya yin komai ba dangane kisan gillan dake faruwa a benue,taraba,adamawa,borno,da kuma wasu sassa afadin kasar,da kuma nuna banbancin da Gwamnatin tarayya take yi.
Kuwa duk munsan cewa apc tana tsoron fuskantan duk wani zaben day ake zuwa nan gaba,dan yan najeriya sunsan cewa sune sanadiyar gurba cewar tattalin arzikin kasar.
Yan najeriya kuma suna jin zafin irin wannan hanyan da suka bi wajen zaben wa yanda suka jawo musu tsadar rayuwa,hakan kuma yanada nasaba da irin mulkin da APC takeyi.
APC ta shiga wani haline saboda yan najeriya sunriga sun canja ra’ayin su,acewar su pdp zasu zaba,wannan sabon tunanin day an nageria sukayi shine yake nun ace wa sun gaji da apc,kuma pdp tafara dawowa,duba da zaben sanata a osun da kuma zaben kananan hukumomi a ekiti da jihar delta.
Yau APC tasan cewa baza ta cin zaben zalinci ba kamar yadda tayi a 2015, ta hanyan karya da kuma yaudara,alkawari aikin da babushi,abinci a makaranru,kyautan gidaje,rage kudin fetir,da kuma karya dalla daya zuwa naira daya da wasu alkawaririka da sukayi,a cewar PDP.
No comments