Labarai Da Dumi Dumi

MACE DA SON KWALLIYA BA KAMAR MAZA BA

Wajen kwalliya mata sunfi taka rawa da kuma bada mahimmanci wajen bukasa harkan kwalliya,a kowa ni lokaci mata suna sun yin ado domin suburge Samari,amma saidai dama su akafi sani da jin dadi,kwalliya da yanga,mata na son yin amfani da kayan aro da kuma son fitowa fiye dasauran.

Saboda son kwalliya hakan ya kansa su hana mazajen su kwanciyar hankali da kuma rabuwa da Masoyansu,wannan karami ne daga cikin aikinsu,kamar Atamfa  yakan sa mace tarinka jin kanta kamar wata Sarauniya.
Bayan tafito daga wanka,tasha fa mai,saita je gaban madubi sai taga kamar bawata bayan ita,amma kuma badaga nan abin yakeba dan saita bata Lokaci kimanin awa daya zuwa biyu tana fama da kwalliya,mace mai son kwalllaya takan samu masoya, fiye da wanda batayi,mata har gasa sukeyi wajen gaye,bakamar yanda maza sukeyi ba,Ko nawa ta samu tana sauri ta siyo atamfa takaima tela dan yamata dinkin kece raini.

Naga Mata da son gidan biki,suna da taro,Mata harso suke ace za’ayi anko dan su fara adashi saboda kada ace an huceta,wata Macen zata iya rabuwa da saurayinta dan bai Mata kayan anko ba,kirarin Mata adon gari ya dace dasu saboda dazarar Mace tashigo waje saidai kaka Maza na kekawa dasu ga wacce take zuwa dan kamshin turarenta ya rigata zuwa,wannan ai sai Mata

No comments