Labarai Da Dumi Dumi

WHATSAPP: A YANZU ZAKU IYA TILASTAWA MAHALARTA KUNGIYOYIN TATTAUNAWA SUYI SHIRU A LOKACIN TATTAUNAWA.



sabon manhajin sadarwa na whatsApp

Mahukunta na kungiyoyin tattaunawa sun kara samun wata dama ta inda zasu iya tilastawa mahalarta zaurukan tattaunawa da su yi shiru, sai dai kawai su karanta sakonni.



Idan ka kasance jagoran tattaunawa, to kai kadai ka ke da damar aika sako, ragowar mahalarta kuma sai dai su karanta saƙo ba tare da tura sako ba.


A wannan sabon tsari da akai wa lakabi da "Ƙuntataccen Ƙungiya", mai jagorancin tattaunawa ne kawai yake da ikon kunna shi. 


Idan aka kunna wannan tsari to zai hana duk ayyukan sadarwar ga waɗanda ba jagorori ba, zai hana su iya aika saƙonnin rubutu, hotuna, bidiyo, takardu ko saƙon murya, ko raba wurin su ba.


Jagorori a halin yanzu, za su iya ci gaba da hira kamar yadda suka saba. Ragowar mahalarta kuma sai dai kawai su karanta saÆ™onnin. 


Idan wanda ba mai gudanarwa yana son yin magana, zai iya yin haka ta amfani da maɓallin "Message Admin", daga nan sakon zai bukaci amincewar mai gudanarwa kafin sakon ya bayyana ga sauran yan kungiya.


Wannan sabuwar siffar da ta zo a sabon manhajin sadarwa na whatsapp mai suna "beta versions" zatai aiki ne a wayoyi masu dauke da iOS da kuma Android.

No comments