MAI HORASWA NA KUNGIYAR KWALLON KAFA TA CHELSEA WATO CONTE YACE BASHIDA SHIRIN BARIN KUNGIYAR A MATSAYIN ME HORASWA
Makomar Antonio Conte zata iya kawo babbar muhawara, amma mai horaswar yace bashi da niyyar barin kungiyar.
Duk da taimakawa kungiyar kwallon kafar da lashe gasar premier league a shekararsa ta farko a kungiyar da yayi, an ta tambayar mai horaswar akan makomarsa a kungiyar watanni kusa kusa da suka gabata, duk da wadannan jita jitar da take ta yaduwa ana tunanin zai iya barin kungiyar kafin kwantaraginsa ya kare a watan yuni na shekara ta 2019.
A farkon wannan watan, Conte ya nuna rashin jin dadinsa na yadda kungiyar kwallon kafar take saya da sayarwar 'yan wasa, yana cewa "a tarihina mafi yawanci ba'a fiye kawomin 'yan wasan da na tambaya inaso ba" wannan shi yasa "yake karewa a kulublikan da basa biya masa bukata"
No comments