Labarai Da Dumi Dumi

SABON TSARIN MANHAJAR SADA ZUMUNTA NA WHATSAPP ZAI BAKU DAMAR CIRE JAGORORIN TATTAUNAWA WATO "GROUP ADMINS" A TURANCE DAGA MATSAYIN JAGORORI

Sabon manhajar whatsapp, whatsapp
sabon tsarin manhajar sada zumunta na WhatsApp.

Amfani da wannan sabon tsari a kan wani zai juya su daga matsayin masu halartar tattaunawar maimakon masu ikon gudanar da tattaunawa.

Sabon WhatsApp din ya fara bawa masu amfani da shi damar "watsi" da masu gudanarwa da tattaunawar kungiya wato "group admins" a turance.

Manhajar WhatsApp din an gina shi ne da wani sabon fasali, wanda ake kira "Ƙaddamar da Gudanarwa", wanda zai sa wani jagoran tattaunawa wato "group admin" ya cire wani jagoran wannan tattaunawar shi kuma ya cigaba da kasancewa jagora mai rike da ikon tattaunawa.

Idan kun yi amfani da wanan sabon tsarin akan wani jagoran tattaunawa to zai rasa duk damar da yake da ita a matsayin sa na jagora kuma zai koma daidai da sauran 'yan kungiya.

Duk wanda yake son amfani da wannan sabon tsarin to dole sai ya kasance jagoran tattaunawa kuma sai daga martabar manhajar WhatsApp din sa zuwa sabon tsarin wanda akai wa lakabi da "beta version".

wannan sabon tsari tuni ya fara aiki ga masu amfani da wayoyi kirar android, a yayin masu amfani da wayoyi kirar Iphone nan ba da jimawa ba zasu fara morar wannan tsari.

No comments