Labarai Da Dumi Dumi

MUNA MARABA DA ZUWAN KWANKWASO – GANDUJE

Muna maraba da zuwan Kwankwaso – Ganduje
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya na maraba da zuwan tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso Kano domin gangamin siyasa, amma bai amince da tashin hankali ba.
Rahotanni na baiyana cewa tsohon gwamnan wanda yanzu shi ne sanatan Kano ta tsakiya na shirin zuwa Kano ranar 31 ga Janairu domin kaddamar da ‘yan takarar zaben kananan hukumomi.
Kowanne daga cikin tsagin Kwankwasiyya da Gandujiyya dai sun fitar da ‘yan takarar shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a karkashin tutar jam’iyyar APC.
Hakan ya jawo cece-kuce tsakanin bangarorin siyasar Kano dangane da zuwan da Sanata Kwankwaso zai yi.
Sai dai gwamna Ganduje ta bakin kwamishinansa na yada labarai Muhammad Garba ya musanta cewa akwai wani shiri da yake yin a hana Kwankwaso gudanar da taronsa a Kano.
A cewar Muhammad Garba a shirye Ganduje yake ya karbi Kwankwaso kamar yadda yake karbar duk wani babban bakon da ya ziyarci Kano.
Kwamishinan ya ce abinda gwamnati ba zata amince da shi ba shi ne tashin hankali.

No comments