DUBUN WANI MAI GARKUWA DA MUTANE TA CIKA
DUBUN WANI MAI GARKUWA DA MUTANE TA CIKA.
Wannan Bafilatanin sunansa Ibrahim Umar, da aka fi Sani da Oro. Yaro ne dan shekara 20 Kuma shugaban "gungun", wani bangare da Suke satar mutane Akan hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kuma Dajin Zamfara. Da bakinsa ya Gaya cewa ya kashe mutane goma, yayin wannan ta'addancin nasa. Kuma duk Wanda ya kashe sai ya sha jininsa.
Ya tabbatar da cewa in ya sace Mutum Yana Karbar kudin fansa daga Naira milyan 10 zuwa 8 5 akalla milyan biyu. An tambayeshi ko ina kudin, sai yace ya sha giya ya Kuma baiwa Karuwai sauran. Sau tari kuma yace in yakama Mutum, kashewa yake, sannan ya Kira yan Uwan mutumin sukawo kudin fansa. In an kawo kuma, ya sake yin garkuwa da Wanda ya kawo. Shima sai an fa she shi
Yau dai dubunsa da na wasu daga cikin yaransa ta chika. Yan sandan Najeriya na musamman dake karkashin ofishin sufeta janar wato IGP INTELLIGENT RESPONCE TEAM TARE DA HADIN GWIWAR YANSANDA MASU YAKI DA YAN FASHI WATO FEDERAL SARS SUN KAMASU, A ganin Ku me ya dace a masu?
No comments