Labarai Da Dumi Dumi

KISAN GILLA A BENUE: GWAMNA LALONG YA BADA HAKURI

KISAN GILLA A BENUE: GWAMNA LALONG YA BADA HAKURI

Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong ya nemi gafarar gwamnatin jihar Benue da Nigeria Baki daya, akan wasu kalamai da yayi lokacin da wasu ba’a tantance su wanene sukayi kisan gilla a garin ba, suka kasha mutane sama da saba’in a kidayar yan agajin gaggawa. Gwamna Lalong ya ja kunnan Gwamnan jihar Benue wata Samuel Ortom na Benue akan kaddamar da kudirin san a hana kiwan shanu a jihar sa, wadan hakan zai janyo kasha kashen rayuka masu yawa.
Wannan kalaman da Gwamnan Jihar Filato yayi a lokacin da ya fito daga fadar Shugaban kasa wato Muhammadu Buhari ta jawo cecekuce ma banbanta a yanar gizo, akan cewa gwamna lalong na goya bayan kisan gilla da ake tunanin Fulani ne kukayi.

Satin day a gabata Lalong ya kira yan jarida ya fada musu cewa wannan maganar da yi a kwana kin baya bazai haifar dad a mai ido ba. Lalong ya mika ta’aziyyar shi zuwa ga mutanen Benue da Nigeria baki daya na wannan rashi da sukayi. Lalong ya kara da cewa Benue da Nassarawa dukka a Jikin Filato aka cire su, sannan kuma duk suna alkarya daya ne wato Arewa ta Tsakiya, dole ya nuna damuwan shi a duk wani abu day a faru dasu, haka shima idan abu ya faru das hi zasu nuna nasu damuwa.

Sannan ya kara da cewa Filato ba Fada take da Benue ko Nassarawa ba, saboda abu daya ne ya kafa su, kuma dukkan su tsintsiya ne madaurin ki daya.

Ya kara da cewa, yana kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari day a kawo karshen wannan Rigimar da take barkewa tsakanin Makiyaya da Manoma, Domin Najeriya ta zauna Lafiya.


No comments