Labarai Da Dumi Dumi

MAHADI ZAI BAYYANA A KANO - KWANKWASIYYA MOVEMENT

A yayin da Kano take kokarin yin taro, na shigowar tsohon Gwamnan Jihar wato Dr. Rabiu Musa Kwankwaso domin kaddamar da kudirin sa na yin takarar shugaba kasar Najeriya ranar 30/01/2018, mutane da dama suna ta yinkurin ganin wani falala wannan Sanata zai kawo idan har ya shigo cikin Garin Kano, bayan ziyarar da Shugaban Kasar Najeriya ya kawo a shekarar da ta gabata.
Anyi ma wannan zuwan sanata da lakabi "Mahadi Zai Bayyana".
G36 Kwankwasiyya Movement, Kwankwasiyya Amana, Kwankwasiyya Nationwide da dai sauran su, su sukayi wannan hada kan wannan gangami
A wata majiyar kuma Sanatoci 36, da kuma wakilai na taraiya guda 96 ne zasu rako Kwankwaso wannan taro.

No comments